Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 10:9-13-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9-13. Wajen Lawiyawa kuwa, su neYeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi daga zuriyar Henadad da Kadmiyel.'Yan'uwansu kuwa su ne Shebaniya, da Hodiya,Kelita, da Felaya, da Hanan,Mika, da Rehob, da Hashabiya,Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,Hodiya, da Bani, da Beninu.

14-27. Shugabannin jama'a kuwa, su ne Farosh, da Fahat-mowab,Elam, da Zattu, da Bani,Bunni, da Azgad, da Bebai,Adonaija, da Bigwai, da Adin,Ater, da Hezekiya, da Azzur,Hodiya, da Hashum, da Bezai,Harif, da Anatot, da Nebai,Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa,Felatiya, da Hanan, da Anaya,Hosheya, da Hananiya, da Hasshub,Hallohesh, da Filha, da Shobek,Rehum, da Hashabna, da Ma'aseya,Ahaija, da Hanan, da Anan,Malluki, da Harim, da Ba'ana.

28. Jama'ar Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa, da ma'aikatan Haikali, da dukan waɗanda suka ware kansu daga sauran al'umman waɗansu ƙasashe, domin su bi dokokin Allah, su da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, da dai duk waɗanda suke da sani da fahimta,

29. suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu.

Karanta cikakken babi Neh 10