Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 7:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya maƙiyina, kada ka yi murna akaina,Gama sa'ad da na fāɗi, zan tashikuma.Sa'ad da na zauna cikin duhu,Ubangiji zai haskaka ni.

9. Zan ɗauka fushin Ubangiji ne,Gama na yi masa zunubi,Sai lokacin da ya ji da'awata,Har ya yanke mini shari'a.Zai kawo ni zuwa wurin haske,Zan kuwa ga cetonsa.

10. Sa'an nan maƙiyina wanda suke ce mini,“Ina Ubangiji Allahnka?”Zai gani, ya kuma ji kunya.Idanuna za su gan shi lokacin da akatattake shiKamar taɓo a titi.

11. Za a faɗaɗa iyakarkaA ranar da za a gina garunka.

12. A waccan rana mutane za su zowurinka,Daga Assuriya har zuwa Masar,Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis,Daga teku zuwa teku, daga dutsezuwa dutse.

Karanta cikakken babi Mika 7