Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 7:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. A waccan rana mutane za su zowurinka,Daga Assuriya har zuwa Masar,Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis,Daga teku zuwa teku, daga dutsezuwa dutse.

13. Duniya kuwa za ta zama kufai,Saboda mazaunan da suke cikinta,Saboda hakkin ayyukansu.

14. Sai ka yi kiwon mutanenka dasandanka,Wato garken mallakarka,Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmiA tsakiyar ƙasa mai albarka.Bari su yi kiwo cikin Bashan daGileyadKamar a kwanakin dā.

15. “Zan nuna muku abubuwa masubanmamaki,Kamar a kwanakin da kuka fitoƙasar Masar.”

16. Al'umman duniya za su gani,Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka.Za su sa hannuwansu a baka,Kunnuwansu za su kurmance.

17. Za su lashi ƙura kamar maciji daabubuwa masu rarrafe,Za su fito da rawar jiki daga wurinmaɓuyarsu,Da tsoro za su juyo wurin UbangijiAllahnmu,Za su ji tsoronka.

18. Akwai wani Allah kamarka, mai yafemugunta,Mai kawar da laifin ringingādonsa?Ba ya riƙon fushi har abada, gamashi mai alheri ne.

19. Zai sāke jin juyayinmu,Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashinƙafafunsa.Za ka jefar da zunubanmu a cikinzurfin teku.

20. Za ka nuna wa Yakubu aminci,Ga Ibrahim kuma madawwamiyarƙauna,Kamar yadda ka rantse wakakanninmuTun a zamanin dā.

Karanta cikakken babi Mika 7