Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 7:12-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. A waccan rana mutane za su zowurinka,Daga Assuriya har zuwa Masar,Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis,Daga teku zuwa teku, daga dutsezuwa dutse.

13. Duniya kuwa za ta zama kufai,Saboda mazaunan da suke cikinta,Saboda hakkin ayyukansu.

14. Sai ka yi kiwon mutanenka dasandanka,Wato garken mallakarka,Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmiA tsakiyar ƙasa mai albarka.Bari su yi kiwo cikin Bashan daGileyadKamar a kwanakin dā.

15. “Zan nuna muku abubuwa masubanmamaki,Kamar a kwanakin da kuka fitoƙasar Masar.”

16. Al'umman duniya za su gani,Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka.Za su sa hannuwansu a baka,Kunnuwansu za su kurmance.

Karanta cikakken babi Mika 7