Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 6:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya kai mutum, ya riga ya nunamaka abin da yake mai kyau.Abin da Ubangiji yake so gare ka,shi neKa yi adalci, ka ƙaunaci aikataalheri,Ka bi Allah da tawali'u.

9. Ubangiji yana kira ga birnin.Hikima ce ƙwarai a ji tsoronsunanka.“Ki ji ya kabila, wa ya sa mikilokacinki?

10. Ba zan manta da dukiya ta muguntaa gidan mugu ba,Ba kuwa zan manta da bugaggenmudun awo ba.

11. Zan kuɓutar da mutum mai ma'aunina cutaDa ma'aunin ƙarya?

12. Attajiran birnin sun cika zalunci,Mazaunansa kuwa maƙaryata ne,Harshensu na yaudara ne.

13. Domin haka zan buge ku da ciwo,In maishe ku kufai sabodazunubanka.

14. Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba,Yunwa za ta kasance a cikinku,Za ku tanada, amma ba zai tanaduba,Abin da kuma kuka tanada zan baiwa takobi.

15. Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba.Za ku matse 'ya'yan zaitun, ammaba za ku shafa mansa ba,Za ku kuma matse 'ya'yan inabi,amma ba za ku sha ruwansa ba.

16. Domin kun kiyaye dokokin Omri,Kun bi halin gidan Ahab,Kun kuma bi shawarwarinsu.Domin haka zan maishe ku kufai,In mai da ku abin dariya,Za ku sha raini a wurin mutanena.”

Karanta cikakken babi Mika 6