Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 6:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ubangiji zai yi murna da ragunadubbaiKo kuwa da kogunan mai dubbai?Zan ba da ɗan farina ne donlaifina?Ko kuwa zan ba da 'ya'yana sabodazunubina?

8. Ya kai mutum, ya riga ya nunamaka abin da yake mai kyau.Abin da Ubangiji yake so gare ka,shi neKa yi adalci, ka ƙaunaci aikataalheri,Ka bi Allah da tawali'u.

9. Ubangiji yana kira ga birnin.Hikima ce ƙwarai a ji tsoronsunanka.“Ki ji ya kabila, wa ya sa mikilokacinki?

10. Ba zan manta da dukiya ta muguntaa gidan mugu ba,Ba kuwa zan manta da bugaggenmudun awo ba.

11. Zan kuɓutar da mutum mai ma'aunina cutaDa ma'aunin ƙarya?

12. Attajiran birnin sun cika zalunci,Mazaunansa kuwa maƙaryata ne,Harshensu na yaudara ne.

13. Domin haka zan buge ku da ciwo,In maishe ku kufai sabodazunubanka.

14. Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba,Yunwa za ta kasance a cikinku,Za ku tanada, amma ba zai tanaduba,Abin da kuma kuka tanada zan baiwa takobi.

Karanta cikakken babi Mika 6