Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 5:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Za su mallaki ƙasar Assuriya datakobi,Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod dazararren takobi,Zai cece mu daga hannunBa'assuriye,Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmuyaƙi,Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.

7. Sa'an nan ringin Yakubu zai zamarwa mutaneKamar raɓa daga wurin Ubangiji,Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire,Wanda ba ya jinkiri ko ya jiramutane.

8. Ringin Yakubu kuma zai zamar waal'umman duniya,Kamar yadda zaki yake a tsakaninnamomin jeji,Kamar kuma yadda zaki yake atsakanin garkunan tumaki,Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakantattaka,Ya yi kacakaca da su,Ba wanda zai cece su.

9. Za a ƙarfafa hannunka a kanmaƙiyanka,Za a datse maƙiyanka duka.

10. “A wannan rana, ni Ubangiji na ce,Zan kashe dawakanku, in hallakakarusanku.

11. Zan shafe biranen ƙasarku,In rushe garunku.

12. Zan kawar da maita daga ƙasarku,Ba za ku ƙara samun bokaye ba.

13. Zan sassare siffofinku daginshiƙanku,Ba za ku ƙara sunkuya wa aikinhannuwanku ba.

14. Zan tumɓuke gumakan nan Ashtarotdaga cikinku,Zan hallaka biranenku.

15. Da fushi da hasala zan yi sakayyaA kan al'umman da ba su yi biyayyaba.”

Karanta cikakken babi Mika 5