Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 3:5-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ga abin da Ubangiji ya ce a kanannabawan da suka bi damutanensa a karkace,Waɗanda suke cewa, “Salama,”sa'ad da suke da abinci,Amma sukan kai yaƙin shahadaGa wanda bai ba su abin sawa a bakaba.

6. Saboda haka kome zai zama dareda duhu, ba wahayi ko duba.Rana za ta fāɗi a kan annabawa,Yini zai zama musu duhu baƙiƙirin.

7. Masu gani za su sha kunya,Masu duba kuwa za su ruɗe,Dukansu za su rufe bakinsu,Gama ba amsa daga wurin Allah.

8. Amma ni ina cike da iko,Da Ruhun Ubangiji,Da shari'a da ƙarfin hali,Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,Isra'ila kuma da zunubinsa.

Karanta cikakken babi Mika 3