Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 1:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. “Domin haka zan mai da Samariyajujin kufai a karkara,Wurin dasa kurangar inabi.Zan zubar da duwatsunta a cikinkwari,In tone harsashin gininta.

7. Za a farfashe dukan siffofinta nazubi,Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,Zan lalatar da gumakanta duka,Gama ta wurin karuwanci ta samosu,Ga karuwanci kuma za su koma.”

8. Mika ya ce, “Saboda wannan zan yibaƙin ciki, in yi kuka,Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.Zan yi kuka kamar diloli,In yi baƙin ciki kamar jiminai.

9. Gama raunin Samariya, ba yawarkuwa,Gama ya kai Yahuza,Ya kuma kai ƙofar jama'ata aUrushalima.”

Karanta cikakken babi Mika 1