Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 1:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. “Domin haka zan mai da Samariyajujin kufai a karkara,Wurin dasa kurangar inabi.Zan zubar da duwatsunta a cikinkwari,In tone harsashin gininta.

7. Za a farfashe dukan siffofinta nazubi,Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,Zan lalatar da gumakanta duka,Gama ta wurin karuwanci ta samosu,Ga karuwanci kuma za su koma.”

8. Mika ya ce, “Saboda wannan zan yibaƙin ciki, in yi kuka,Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.Zan yi kuka kamar diloli,In yi baƙin ciki kamar jiminai.

9. Gama raunin Samariya, ba yawarkuwa,Gama ya kai Yahuza,Ya kuma kai ƙofar jama'ata aUrushalima.”

10. Kada a faɗe shi a Gat,Sam, kada a yi kuka.Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.

11. Ku mazaunan Shafir, ku wuceabinku da tsiraici da kunya.Mazaunan Za'anan ba su tsira ba.Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zaitumɓuke harasashin gininki.”

12. Mutanen Marot sun ƙosa su gaalheri,Amma masifa ta zo ƙofarUrushalima daga wurin Ubangiji.

13. Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wadawakai karusai,Gama ku kuka fara yin zunubi aSihiyona,Gama an iske laifofin Isra'ilacikinku.

14. Domin haka sai ku ba Moreshet-gatguzuri,Mutanen Akzib za su yaudarisarakunan Isra'ila.

15. Ku mazaunan Maresha, Ubangiji zaikawo wanda zai ci ku da yaƙi,Darajar Isra'ila za ta shigaAdullam.

16. Ku aske kanku saboda ƙaunatattun'ya'yanku.Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamarungulu,Gama 'ya'yanku za su tafi bautartalala.

Karanta cikakken babi Mika 1