Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 1:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.

2. Dukanku ku ji, ku al'ummai!Ki kasa kunne, ya duniya, da dukanabin da yake cikinki.Bari Ubangiji AllahDaga Haikalinsa mai tsarki ya zamashaida a kanku.

3. Ga shi, Ubangiji yana fitowa dagawurin zamansa,Zai sauko, ya taka kan tsawawanduwatsun duniya.

4. Duwatsu za su narke aƙarƙashinsa,Kwaruruka za su tsattsage kamarkakin zuma a gaban wuta,Kamar ruwa yana gangarowa dagatsauni.

5. Duk wannan kuwa saboda laifinYakubu ne,Da laifin Isra'ila.Mene ne laifin Yakubu?Ashe, ba bautar gumaka da zaluncinda ake yi a Samariya ba?Mene ne kuma laifin Yahuza?Ashe, ba bautar gumaka da zaluncinda ake yi a Urushalima ba?

6. “Domin haka zan mai da Samariyajujin kufai a karkara,Wurin dasa kurangar inabi.Zan zubar da duwatsunta a cikinkwari,In tone harsashin gininta.

7. Za a farfashe dukan siffofinta nazubi,Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,Zan lalatar da gumakanta duka,Gama ta wurin karuwanci ta samosu,Ga karuwanci kuma za su koma.”

Karanta cikakken babi Mika 1