Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 1:16-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. “Ina kuka saboda waɗannan abubuwa,Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna.Gama mai ta'azantar da ni,Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni.'Ya'yana sun lalace,Gama maƙiyi ya yi nasara!”

17. Sihiyona tana miƙa hannuwanta,Amma ba wanda zai ta'azantar da ita.Gama Ubangiji ya umarci maƙwabtan Yakubu su zama maƙiyansa.Urushalima kuma ta zama ƙazantacciya a tsakaninsu.

18. “Abin da Ubangiji ya yi daidai ne,Gama ni na ƙi bin maganarsa,Ku ji, ya ku jama'a duka,Ku dubi wahalata,'Yan matana da samarina,An kai su bauta!

19. “Na kira masoyana, amma suka yaudare ni,Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallakaSaboda neman abincin da za su ci su rayu.

20. “Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala,Raina yana cikin damuwa,Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata.A titi takobi yana karkashewa,A gida kuma ga mutuwa.

21. “Sun ji yadda nake nishi,Ba mai ta'azantar da ni.Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki,Suna kuwa murna da ka yi haka.Ka kawo ranan nan da ka ambata,Domin su ma su zama kamar yadda nake.

22. “Ka sa mugayen ayyukansu su bayyana a gabanka,Sa'an nan ka hukunta su kamar yadda ka hukunta ni saboda dukan laifofina.Gama nishe-nishena sun yi yawa.Zuciyata kuma ta karai.”

Karanta cikakken babi Mak 1