Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 8:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sai ku lura, ku aikata dukan umarnan da na umarce ku da su don ku rayu, ku riɓaɓɓanya, ku shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.

2. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.

3. Ya koya muku tawali'u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.

4. A shekarun nan arba'in tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba.

5. Kun san wannan a zuciyarku, wato kamar yadda mutum yakan yi wa ɗansa tarbiyya, haka kuma Ubangiji Allahnku yake yi muku tarbiyya.

6. Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa.

7. Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu.

8. Ƙasa mai alkama, da sha'ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma.

9. Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.

10. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”

11. “Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau.

Karanta cikakken babi M. Sh 8