Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 7:6-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa.

7. “Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al'ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al'ummai.

8. Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar.

9. Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa.

10. Amma a fili Ubangiji yakan yi ramuwa a kan maƙiyansa, yakan hallaka su. Ba zai yi jinkirin yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.

11. Saboda haka, sai ku kiyaye umarnai, da dokoki, da farillai ku aikata su, wato waɗanda nake umartarku da su yau.”

12. “Idan za ku saurari waɗannan farillai, ku kiyaye su, sai Ubangiji Allahnku ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku, ya kuma ƙaunace ku.

13. Ubangiji zai ƙaunace ku, ya sa muku albarka, ya riɓaɓɓanya ku. Zai sa wa 'ya'yanku albarka, ya yalwata amfanin gonarku, da hatsinku, da inabinku, da manku, da garken shanunku, da 'yan ƙananan garkenku a ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.

14. Za ku fi kowace al'umma samun albarka. Ba za a iske mutum ko mace marar haihuwa a cikinku ba, ko a cikin garkenku.

15. Ubangiji zai kiyaye ku daga dukan cuce-cuce. Ba zai wahalshe ku da mugayen cuce-cuce na Masar ba, waɗanda kuka sani, amma zai wahalar da duk maƙiyanku da waɗannan mugayen cuce-cuce.

16. Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.

17. “Ya yiwu ku ce a zuciyarku, ‘Waɗannan al'ummai sun fi mu yawa, ta ƙaƙa za mu iya ƙorarsu?’

18. Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya yi da Fir'auna da dukan Masarawa.

19. Ku tuna kuma da wahalar da kuka gani da idonku, da alamu, da mu'ujizai, da dantse mai iko mai ƙarfi wanda Ubangiji Allahnku ya fito da ku. Haka nan kuma Ubangiji Allahnku zai yi da dukan al'umman nan da kuke jin tsoronsu.

20. Banda wannan kuma Ubangiji Allahnku zai aiko da zirnako a cikinsu su hallaka sauran da suka ragu, suka ɓuya.

21. Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana.

22. Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al'ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku.

Karanta cikakken babi M. Sh 7