Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 7:20-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Banda wannan kuma Ubangiji Allahnku zai aiko da zirnako a cikinsu su hallaka sauran da suka ragu, suka ɓuya.

21. Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana.

22. Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al'ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku.

23. Ubangiji Allahnku zai bashe su a gare ku, zai firgitar da su har ya hallakar da su.

24. Zai ba da sarakunansu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Ba wanda zai iya tasar muku har kun ƙare su.

25. Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu.

26. Kada ku kawo abin ƙyama a gidajenku don kada ku zama abin ƙyama kamarsa. Lalle sai ku ƙi shi, ku ji ƙyamarsa, gama haramtacce ne.”

Karanta cikakken babi M. Sh 7