Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 5:23-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Sa'ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina,

24. suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu.

25. Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu.

26. Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?

27. Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’

28. “Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama'an nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne.

29. Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada.

30. Tafi, ka faɗa musu su koma cikin alfarwansu.

Karanta cikakken babi M. Sh 5