Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 33:14-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Da kyawawan kyautan da rana take bayarwa,Da kyawawan kyautan da watanni suke bayarwa,

15. Da abubuwa mafi kyau na duwatsun dā,Da kyawawan kyautai na madawwaman tuddai.

16. Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta,Da alherin wanda yake zaune a jeji.Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu,A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin 'yan'uwansa.

17. Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take,Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke,Da su yake tunkwiyin mutane,Zai tura su zuwa ƙurewar duniya,Haka fa rundunan Ifraimu za su zama,Haka kuma dubban Manassa za su zama.”

18. A kan Zabaluna ya ce,“Ka yi murna da tafiye-tafiyenka, ya Zabaluna,Kai kuma Issaka, cikin alfarwanka.

19. Za su kira mutane zuwa dutse,Can za su miƙa hadayu masu dacewa,Gama za su ɗebo wadatar tekuna,Da ɓoyayyun dukiyar yashi.”

20. A kan Gad, ya ce,“Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad,Gad yana sanɗa kamar zaki,Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai.

21. Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau,Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba.Ya zo wurin shugabannin mutane,Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji,Ya kiyaye farillansa.”

22. A kan Dan, ya ce,“Dan ɗan zaki ne,Mai tsalle daga Bashan.”

23. A kan Naftali, ya ce,“Ya Naftali, ƙosasshe kake da alheri,Cike kake da albarkar Ubangiji.Sai ka mallaki tafki da wajen kudu.”

24. A kan Ashiru, ya ce,“Ashiru mai albarka ne fiye da sauran 'yan'uwansa,Bari ya zama abin ƙauna ga 'yan'uwansa,Ya kuma tsoma ƙafarsa cikin mai.

25. Kurfanka na baƙin ƙarfe ne da tagulla,Ƙarfinka ba zai rabu da kai ba muddin ranka.”

26. “Babu wani kamar Allahn Yeshurun,Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka,Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa.

27. Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka,Madawwaman damatsansa suna tallafarka,Yana kore maka maƙiyanka,Ya ce, ‘Ka hallaka su!’

28. Da haka Isra'ila yana zaune lafiya,Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗaiA ƙasa mai hatsi da ruwan inabi,Wurin da raɓa take zubowa daga sama.

29. Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila!Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta?Ubangiji ne garkuwarku,Shi ne kuma takobinku mai daraja.Magabtanku za su yi muku fādanci,Amma ku za ku tattake masujadansu.”

Karanta cikakken babi M. Sh 33