Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 33:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ya Ubangiji ka inganta jaruntakarsu,Ka karɓi aikin hannuwansu,Ka murƙushe ƙarfin abokan gābansu,Da waɗanda suke ƙinsu don kada su ƙara tashi.”

12. A kan Biliyaminu, ya ce,“Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne,Yana zaune lafiya kusa da shi,Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini,Yana zaune a kan kafaɗunsa.”

13. A kan Yusufu, ya ce,“Ubangiji ya sa wa ƙasarsa albarka,Da kyawawan kyautai daga sama, da raɓa,Da ruwan da yake a ƙasa,

14. Da kyawawan kyautan da rana take bayarwa,Da kyawawan kyautan da watanni suke bayarwa,

15. Da abubuwa mafi kyau na duwatsun dā,Da kyawawan kyautai na madawwaman tuddai.

16. Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta,Da alherin wanda yake zaune a jeji.Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu,A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin 'yan'uwansa.

17. Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take,Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke,Da su yake tunkwiyin mutane,Zai tura su zuwa ƙurewar duniya,Haka fa rundunan Ifraimu za su zama,Haka kuma dubban Manassa za su zama.”

Karanta cikakken babi M. Sh 33