Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 32:7-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Ku fa tuna da kwanakin dā,Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,

8. Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu,Sa'ad da ya raba 'yan adam,Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.

9. Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa,Yakubu shi ne rabon gādonsa.

10. “Ya same shi daga cikin hamada,A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.Ya kewaye shi, ya lura da shi,Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.

11. Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta,Tana rufe da 'yan tsakinta,Ta buɗe fikafikanta, ta kama su,Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.

12. Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi,Ba wani baƙon allah tare da shi.

13. “Ya sa shi ya hau kan tuddai,Ya ci amfanin ƙasa,Ya sa shi ya sha zuma daga dutse,Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.

14. Ya sami kindirmo daga shanu,Da madara daga garken tumaki da na awaki,Da kitse daga 'yan raguna, da raguna,Da bijimai, da bunsurai daga Bashan,Da alkama mafi kyau.Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.

15. “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska,Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul.Ya rabu da Allahn da ya yi shi,Ya raina Dutsen Cetonsa.

16. Suka sa shi kishi, saboda gumaka,Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.

17. Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba,Ga gumakan da ba su sani ba,Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya,Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.

18. Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku,Kun manta da Allahn da ya ba ku rai.

19. “Ubangiji ya gani, ya raina su,Saboda tsokanar da 'ya'yansa mata da maza suka yi masa.

20. Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata,Zan ga yadda ƙarshensu zai zama.Gama su muguwar tsara ce,'Ya'ya ne marasa aminci.

21. Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba,Suka tsokani fushina da gumakansu,Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba.Zan tsokane su da wawanyar al'umma.

22. Gama fushina ya kama wuta,Tana ci har ƙurewar zurfin lahira.Za ta cinye duniya da dukan amfaninta,Za ta kama tussan duwatsu.

23. “ ‘Zan tula musu masifu,Zan ƙare kibauna a kansu,

24. Za su lalace saboda yunwa,Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.Zan aika da haƙoran namomi a kansu,Da dafin abubuwa masu jan ciki.

25. Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,A cikin ɗakuna kuma tsoro,Zai hallaka saurayi da budurwa,Da mai shan mama da mai furfura.

Karanta cikakken babi M. Sh 32