Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 32:41-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya,Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci,Zan ɗauki fansa a kan magabtanaZan sāka wa maƙiyana.

42. Zan sa kibauna su bugu da jini,Takobina zai ci nama,Da jinin kisassu da na kamammu,Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.’

43. “Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa,Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu,Zai ɗauki fansa a kan magabtansa,Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”

44. Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama'a.

45. Sa'ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra'ila,

46. ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.

47. Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”

48. A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa,

49. “Ka hau duwatsun Abarim, wato Dutsen Nebo wanda yake a ƙasar Mowab, daura da Yariko, ka duba ƙasar Kan'ana wadda zan ba Isra'ilawa su mallaka.

50. Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan'uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya.

51. Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba.

52. Za ka ga ƙasar da nake ba jama'ar Isra'ila, amma ba za ka shiga cikinta ba.”

Karanta cikakken babi M. Sh 32