Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 32:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,In yabi girman Allahnmu!

4. “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.

5. Sun aikata mugunta a gabansa,Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu,Su muguwar tsara ce, karkatacciya,

6. Haka za ku sāka wa Ubangiji,Ya ku wawaye, mutane marasa hikima?Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba,Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?

7. “Ku fa tuna da kwanakin dā,Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,

8. Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu,Sa'ad da ya raba 'yan adam,Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.

9. Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa,Yakubu shi ne rabon gādonsa.

10. “Ya same shi daga cikin hamada,A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.Ya kewaye shi, ya lura da shi,Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.

11. Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta,Tana rufe da 'yan tsakinta,Ta buɗe fikafikanta, ta kama su,Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.

12. Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi,Ba wani baƙon allah tare da shi.

13. “Ya sa shi ya hau kan tuddai,Ya ci amfanin ƙasa,Ya sa shi ya sha zuma daga dutse,Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.

14. Ya sami kindirmo daga shanu,Da madara daga garken tumaki da na awaki,Da kitse daga 'yan raguna, da raguna,Da bijimai, da bunsurai daga Bashan,Da alkama mafi kyau.Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.

15. “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska,Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul.Ya rabu da Allahn da ya yi shi,Ya raina Dutsen Cetonsa.

16. Suka sa shi kishi, saboda gumaka,Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.

Karanta cikakken babi M. Sh 32