Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 32:19-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. “Ubangiji ya gani, ya raina su,Saboda tsokanar da 'ya'yansa mata da maza suka yi masa.

20. Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata,Zan ga yadda ƙarshensu zai zama.Gama su muguwar tsara ce,'Ya'ya ne marasa aminci.

21. Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba,Suka tsokani fushina da gumakansu,Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba.Zan tsokane su da wawanyar al'umma.

22. Gama fushina ya kama wuta,Tana ci har ƙurewar zurfin lahira.Za ta cinye duniya da dukan amfaninta,Za ta kama tussan duwatsu.

23. “ ‘Zan tula musu masifu,Zan ƙare kibauna a kansu,

24. Za su lalace saboda yunwa,Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.Zan aika da haƙoran namomi a kansu,Da dafin abubuwa masu jan ciki.

25. Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,A cikin ɗakuna kuma tsoro,Zai hallaka saurayi da budurwa,Da mai shan mama da mai furfura.

26. Na ce, “Zan watsar da su,In sa a manta da su cikin mutane.”

27. Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi,Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara.Ai, ni ne na yi wannan.’

28. “Gama su al'umma ce wadda ba ta yin shawara,Ba su da ganewa.

29. Da suna da hikima, da sun gane wannan,Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!

30. Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu,Mutum biyu kuma su kori zambar goma,Sai dai Dutsensu ya sayar da su,Ubangiji kuma ya bashe su?

31. Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne,Ko abokan gabanmu ma sun san haka.

Karanta cikakken babi M. Sh 32