Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 30:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Gama wannan umarni da na yi muku yau, bai fi ƙarfinku ba, bai kuma yi nisa da ku ba.

12. Ba cikin Sama yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai hau zuwa sama, ya sauko mana da shi don mu ji, mu kiyaye?’

13. Ba kuma a hayin teku yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai haye mana wannan teku don ya kawo mana shi don mu ji, mu kiyaye?’

14. Amma umarnin yana kurkusa da ku, yana cikin bakinku da zuciyarku don ku kiyaye shi.

15. “Ga shi yau, na sa rai da nagarta a gabanku, da mutuwa da mugunta.

16. Idan kuka kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, idan kuma kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna yin tafiya cikin tafarkunsa, kuna kiyaye umarnansa, da dokokinsa, da farillansa, to, za ku rayu, ku riɓaɓɓanya, Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.

17. Amma idan zuciyarku ta kangare kun ƙi ku saurara, amma zuciyarku ta janye ku kun yi wa gumaka sujada, kuka bauta musu,

18. to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba.

19. Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la'ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku.

20. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi biyayya da maganarsa, ku manne masa, gama wannan shi ne ranku da tsawon kwanakinku, don ku zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya rantse zai ba kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”

Karanta cikakken babi M. Sh 30