Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 3:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. “A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Haka nan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu.

22. Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.’ ”

23. “Sa'an nan kuma na roƙi Ubangiji, na ce,

24. ‘Ya Ubangiji Allah, kai ne ka fara nuna wa baranka ɗaukakarka da ikonka. Ba wani Allah a Sama ko a duniya da zai aikata ayyuka na banmamaki irin naka.

25. Ka yarje mini, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun, ƙasan nan mai kyau ta tuddai, da Lebanon.’

26. “Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, ‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al'amari.

27. Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba.

28. Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama'ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’

Karanta cikakken babi M. Sh 3