Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 3:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama'arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai.

2. Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama'arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.’

3. “Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai.

4. Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan.

5. Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu.

6. Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara.

Karanta cikakken babi M. Sh 3