Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama'arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai.

2. Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama'arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.’

3. “Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai.

4. Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan.

5. Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu.

Karanta cikakken babi M. Sh 3