Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 28:33-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum.

34. Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata.

35. Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.

36. “Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.

37. Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.

38. “Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye.

39. Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi.

40. Za ku sami itatuwan zaitun ko'ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama 'ya'yan za su kakkaɓe.

41. Za ku haifi 'ya'ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta.

42. Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku.

43. “Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya.

44. Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.

45. “Dukan waɗannan la'anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba.

46. Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada.

47. Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace,

48. domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.

49. Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,

50. al'umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara.

Karanta cikakken babi M. Sh 28