Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 27:8-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.”

9. Sai Musa da Lawiyawan da suke firistoci, suka ce wa Isra'ilawa, “Ku ji. Yau kun zama jama'ar Ubangiji Allahnku.

10. Sai ku saurari muryar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa, da dokokinsa waɗanda muke umartarku da su yau.”

11. A wannan rana kuma Musa ya umarci jama'a, ya ce,

12. “Sa'ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama'a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu.

13. Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la'anta, wato kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali.

14. Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa:

15. “ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

Karanta cikakken babi M. Sh 27