Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 27:11-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. A wannan rana kuma Musa ya umarci jama'a, ya ce,

12. “Sa'ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama'a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu.

13. Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la'anta, wato kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali.

14. Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa:

15. “ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

16. “ ‘La'ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

17. “ ‘La'ananne ne wanda ya ci iyakar maƙwabcinsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

18. “ ‘La'ananne ne wanda ya karkatar da makaho daga hanya.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

19. “ ‘La'ananne ne wanda ya yi wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa ta gaske shari'a ta rashin gaskiya.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

20. “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

21. “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da dabba.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

22. “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

23. “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

24. “ ‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!”

25. “ ‘La'ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’

26. “ ‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”

Karanta cikakken babi M. Sh 27