Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 23:7-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.

8. 'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”

9. “Sa'ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu.

10. Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin.

11. Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa'ad da rana ta faɗi.

12. “Za ku keɓe wani wuri a bayan sansani inda za ku riƙa zagayawa.

13. Sai ku ɗauki abin tona ƙasa tare da makamanku. Lokacin da za ku zagaya garin yin najasa, sai ku tsuguna ku tona rami da abin tona ƙasa sa'an nan ku rufe najasar da kuka yi.

14. Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”

15. “Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa.

16. Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi.

17. “Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.

18. Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa'adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

Karanta cikakken babi M. Sh 23