Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 23:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. “Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.

18. Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa'adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

19. “Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa.

20. Kun iya ba baƙo rance da ruwa, amma kada ku ba danginku rance da ruwa don Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan abin da za ku yi a ƙasar da kuke shiga, ku kuma mallake ta.

21. “Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba.

22. Idan kun nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba.

23. Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi wanda kuka alkawarta.

24. “Sa'ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin 'ya'yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku.

25. Sa'ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”

Karanta cikakken babi M. Sh 23