Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 21:21-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”

22. “Idan mutum ya yi laifin da ya isa mutuwa, aka rataye shi a itace har ya mutu,

23. kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”

Karanta cikakken babi M. Sh 21