Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 20:17-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku,

18. don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.

19. “Sa'ad da kuka kewaye gari da yaƙi, kuka daɗe kuna yaƙi da shi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari har ku lalata su, gama za ku ci amfaninsu. Kada ku sassare su, gama itatuwan da yake cikin saura ba mutane ba ne, da za ku kewaye su da yaƙi.

20. Sai dai itatuwan da kuka sani ba su ba da 'ya'ya, su ne za ku sassare, ku yi kagara da su saboda garin da kuke yaƙi da shi har ku ci garin.”

Karanta cikakken babi M. Sh 20