Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 17:13-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan duk jama'a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”

14. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku don ku mallake ta, ku zauna a ciki, sa'an nan ku yi tunanin naɗa wa kanku sarki, kamar al'umman da suke kewaye da ku,

15. to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba.

16. Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’

17. Kada kuma ya auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace. Kada kuma ya tattara wa kansa kuɗi da yawa.

18. Sa'ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci.

19. Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai,

Karanta cikakken babi M. Sh 17