Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 14:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse.

6. Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa.

7. Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku.

8. Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu.

9. “Daga dukan irin abin da yake zaune a ruwa za ku iya cin duk abin da yake da ƙege da ɓamɓaroki.

10. Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku.

11. “Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye.

Karanta cikakken babi M. Sh 14