Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 14:26-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gafi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.

27. “Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku.

28. A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku.

29. Sa'an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”

Karanta cikakken babi M. Sh 14