Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 8:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Muddin ka kiyaye umarnin sarki gidanka lafiya, mai hikima yakan yi abu, ya kuma san lokacin yi da hanyar da ta dace da yinsa.

6. Akwai lokacin da ya dace, da hanyar da ta dace na yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.

7. Ko ɗaya daga cikinmu ba wanda ya san abin da zai faru, wane ne zai faɗa mana?

8. Ba wanda zai iya hana kansa mutuwa, ko ya dakatar da ranar mutuwarsa. Idan yaƙi ya zo ba makawa, ba yadda za mu yi mu zurare.

9. Na ga wannan duka a sa'ad da nake tunani a kan abubuwan da ake yi a duniyan nan, duniyar da waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.

10. Hakika na ga an kai mugaye an binne, amma a birnin nan inda suka aikata wannan mugun abu, mutane suna yabonsu, amma sun kuma manta da su. Wannan kuma aikin banza ne.

11. Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.

12. Ko da yake mugun mutum ya aikata laifofi sau ɗari, amma kuwa ya rayu, duk da haka na sani idan kana tsoron Allah kome zai tafi daidai.

Karanta cikakken babi M. Had 8