Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutum mai hikima ne kaɗai ya san ainihin ma'anar yadda abubuwa suke. Hikima takan sa shi fara'a, da sakin fuska.

Yi wa Sarki Biyayya

2. Ka kiyaye umarnin sarki saboda alkawarin da ka ɗauka.

3. Sarki yana iya yin kowane abu da ya ga dama, don haka ka guje wa wurin da yake, kada ka zauna a wuri mai hatsari haka.

4. Da iko sarki yake aiki, don haka ba mai iya ce masa, “Don me?”

5. Muddin ka kiyaye umarnin sarki gidanka lafiya, mai hikima yakan yi abu, ya kuma san lokacin yi da hanyar da ta dace da yinsa.

6. Akwai lokacin da ya dace, da hanyar da ta dace na yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.

7. Ko ɗaya daga cikinmu ba wanda ya san abin da zai faru, wane ne zai faɗa mana?

8. Ba wanda zai iya hana kansa mutuwa, ko ya dakatar da ranar mutuwarsa. Idan yaƙi ya zo ba makawa, ba yadda za mu yi mu zurare.

Mugun da Adali

9. Na ga wannan duka a sa'ad da nake tunani a kan abubuwan da ake yi a duniyan nan, duniyar da waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.

10. Hakika na ga an kai mugaye an binne, amma a birnin nan inda suka aikata wannan mugun abu, mutane suna yabonsu, amma sun kuma manta da su. Wannan kuma aikin banza ne.

11. Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.

12. Ko da yake mugun mutum ya aikata laifofi sau ɗari, amma kuwa ya rayu, duk da haka na sani idan kana tsoron Allah kome zai tafi daidai.

13. Ga mugaye ba zai tafi daidai ba, kamar inuwa ransu yake. Za su yi mutuwar ƙuruciya domin ba su da tsoron Allah.

14. Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.

15. Abin da na ce, shi ne mutum ya ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne ya ci, ya sha, ya ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakinsa wanda Allah ya ba shi a wannan duniya.

16. A duk lokacin da nake ƙoƙari in zama mai hikima, in san abin da yake faruwa a duniya, sai na gane, ko da a ce mutum ba zai yi barci ba dare da rana,

17. sam, ba zai taɓa fahimtar abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.