Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 8:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.

12. Ko da yake mugun mutum ya aikata laifofi sau ɗari, amma kuwa ya rayu, duk da haka na sani idan kana tsoron Allah kome zai tafi daidai.

13. Ga mugaye ba zai tafi daidai ba, kamar inuwa ransu yake. Za su yi mutuwar ƙuruciya domin ba su da tsoron Allah.

14. Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.

15. Abin da na ce, shi ne mutum ya ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne ya ci, ya sha, ya ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakinsa wanda Allah ya ba shi a wannan duniya.

16. A duk lokacin da nake ƙoƙari in zama mai hikima, in san abin da yake faruwa a duniya, sai na gane, ko da a ce mutum ba zai yi barci ba dare da rana,

17. sam, ba zai taɓa fahimtar abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.

Karanta cikakken babi M. Had 8