Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 7:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Idan ka riƙe wannan zai amfane ka. Kada ka bar wancan, gama shi wanda yake tsoron Allah zai yi amfani da su.

19. Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.

20. Ba wani mutum a duniyan nan wanda yake aikata abin da yake daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.

21. Kada ka kula da kowane abu da mutane suke faɗa, mai yiwuwa ne ka ji baranka yana zaginka.

22. Kai kanka ka sani sau da yawa kakan zagi waɗansu mutane.

23. Na yi amfani da hikimata don in jarraba wannan duka, domin na ɗaura aniya in zama mai hikima, amma abin ya fi ƙarfina.

24. Wane ne zai iya sanin gaibi? Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa.

25. Amma na duƙufa neman ilimi, ina ta yin nazari, ina nema in san hikima da amsoshin tambayoyina, in kuma san mugunta da wautar dakikanci.

26. Sai na iske wani abu da ya fi mutuwa ɗaci, wato mace wadda ƙaunar da take yi maka za ta kama ka kamar tarko, kamar kuma raga. Rungumewar da za ta yi maka za ta ɗaure ka kamar sarƙa. Wanda Allah yake jin daɗinsa zai tsere mata, amma za ta kama mai zunubi.

27. Haka ne, in ji Mai Hadishi, da kaɗan da kaɗan na gane wannan sa'ad da nake neman amsa.

28. Amsar da nake nema ban samu ba. Na sami mutum ɗaya mai hikima, wato a cikin mutum dubu, amma daga cikin mata ban sami ko ɗaya ba.

29. Wannan ne kaɗai abin da na gane, tsaf Allah ya yi mu, amma mu muka rikitar da kanmu.

Karanta cikakken babi M. Had 7