Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 4:5-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Za su ce, “Wawa ne zai ƙi yin aiki, ya zauna har yunwa ta kashe shi.”

6. Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai, da tafin hannu biyu cike da tashin hankali, harbin iska ne kawai.

7. Na kuma ga wani abu a zaman mutum, wanda bai amfana kome ba,

8. mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.

9. Biyu sun fi ɗaya, gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu.

10. Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya faɗi yana shi kaɗai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi.

11. Idan mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna, amma ƙaƙa mutum ɗaya zai ji ɗumi?

12. Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.

13-14. Mutum yana iya tashi daga matsayin talauci ya zama sarki a ƙasarsa, ko ya fita daga kurkuku ya hau gadon sarauta. Amma lokacin da sarki ya tsufa, idan wautarsa ta hana shi karɓar shawara, bai fi saurayin ɗin da yake talaka mai basira ba.

15. Na yi tunani a kan dukan mutanen da suke zaune a duniyan nan, sai na gane a cikinsu akwai saurayin da zai maye matsayin sarkin.

Karanta cikakken babi M. Had 4