Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 2:21-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Kai ne ka yi aiki da dukan hikimarka, da iliminka, da gwanintarka, amma kuma tilas ka bar shi duka ga wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma bai amfana kome ba, mugun abu ne.

22. Me mutum zai samu daga cikin aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin?

23. Dukan abin da yake yi a kwanakinsa, ba abin da ya jawo masa, sai damuwa da ɓacin zuciya. Da dare ma ba ya iya hutawa. Wannan kuma aikin banza ne duka.

24. Ba abin da ya fi wa mutum kyau fiye da ya ci, ya sha, ya saki jiki, ya ci moriyar aikinsa. Na gane wannan ma daga wurin Allah ne.

25. Ƙaƙa za ka sami abin da za ka ci, ko ka ji daɗin zamanka in ba tare da shi ba?

26. Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.

Karanta cikakken babi M. Had 2