Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 12:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Wato lokacin da rana, da haske, da wata, da taurari za su duhunta, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙar da ruwa.

3. A lokacin nan hannuwanka da suke kāre ka, za su yi makyarkyata, ƙafafunka za su rasa ƙarfi. Haƙora kaɗan za su ragu a bakinka. Idanunka za su duhunta.

4. Bakinka a rufe yake, haƙora ba su tauna abinci. Muryar tsuntsu za ta farkar da kai. Ba za ka iya jin muryar mawaƙa ba.

5. Sa'an nan za ka ji tsoron hawan tudu, tafiya kuma za ta yi maka wuya. Gashin kanka zai furfurce. Za ka ja jikinka. Ba sauran sha'awar mace.Daga nan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna.

6. Hakika, ka tuna da Mahaliccinka kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe, ko tulu ya fashe a bakin rijiya, ko igiya ta tsinke a bakin tafki,

Karanta cikakken babi M. Had 12