Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 12:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin samartakarka kafin mugayen kwanaki da shekaru su zo, da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu.”

2. Wato lokacin da rana, da haske, da wata, da taurari za su duhunta, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙar da ruwa.

3. A lokacin nan hannuwanka da suke kāre ka, za su yi makyarkyata, ƙafafunka za su rasa ƙarfi. Haƙora kaɗan za su ragu a bakinka. Idanunka za su duhunta.

4. Bakinka a rufe yake, haƙora ba su tauna abinci. Muryar tsuntsu za ta farkar da kai. Ba za ka iya jin muryar mawaƙa ba.

Karanta cikakken babi M. Had 12