Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 10:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara.

9. Wanda yake farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni. Wanda kuma yake faskare itace yana cikin hatsarinsu.

10. Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma hikima takan taimake shi ya ci nasara.

11. Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani.

12. Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi.

13. Farkon maganganunsa wauta ne, ƙarshensu kuma mugunta ne da hauka.

14. Wawa ya cika yawan surutu.Wa ya san abin da zai faru nan gaba? Wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?

15. Wahalar wawa takan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.

16. Kaitonki, ya ƙasa wadda sarkinki yaro ne, shugabanninki kuma suna ta shagalinsu tun da safe.

17. Mai farin ciki ce, ke ƙasar da sarkinki mai dattako ne, shugabanninki kuma suka ci a kan kari don su sami ƙarfi, ba domin su bugu ba.

18. Saboda lalaci ɗaki yakan yi yoyo, sai tsaiko ya lotsa.

Karanta cikakken babi M. Had 10