Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Sakamakon Wauta

1. Matattun ƙudaje sukan sa man ƙanshi ya yi wari, haka nan wauta kaɗan takan ɓata hikima da daraja.

2. Zuciyar mai hikima takan kai shi ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan kai shi ga yin mugun abu.

3. Ko lokacin da wawa yake tafiya a hanya, yakan nuna ba shi da hankali, yakan kuma bayyana wa kowa shi wawa ne.

4. Idan mai mulki ya husata da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.

5. Akwai mugunta wadda na gani a duniya, wato kuskuren da masu mulki suke yi.

6. Ana ba wawaye manyan matsayi, attajirai kuwa ana ƙasƙantar da su.

7. Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, shugabanni kuwa suna tafiya a ƙasa kamar bayi.

8. Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara.

9. Wanda yake farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni. Wanda kuma yake faskare itace yana cikin hatsarinsu.

10. Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma hikima takan taimake shi ya ci nasara.

11. Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani.

12. Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi.

13. Farkon maganganunsa wauta ne, ƙarshensu kuma mugunta ne da hauka.

14. Wawa ya cika yawan surutu.Wa ya san abin da zai faru nan gaba? Wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?

15. Wahalar wawa takan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.

16. Kaitonki, ya ƙasa wadda sarkinki yaro ne, shugabanninki kuma suna ta shagalinsu tun da safe.

17. Mai farin ciki ce, ke ƙasar da sarkinki mai dattako ne, shugabanninki kuma suka ci a kan kari don su sami ƙarfi, ba domin su bugu ba.

18. Saboda lalaci ɗaki yakan yi yoyo, sai tsaiko ya lotsa.

19. Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma ba za ka sami ko ɗaya ba, sai idan kana da kuɗi.

20. Kada ka zagi sarki ko a cikin zuciyarka, kada kuma ka zagi mawadaci a cikin ɗakin kwananka, gama tsuntsu zai kai maganarka, wani taliki mai fikafikai zai tone asirinka.