Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 10:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Zuciyar mai hikima takan kai shi ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan kai shi ga yin mugun abu.

3. Ko lokacin da wawa yake tafiya a hanya, yakan nuna ba shi da hankali, yakan kuma bayyana wa kowa shi wawa ne.

4. Idan mai mulki ya husata da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.

5. Akwai mugunta wadda na gani a duniya, wato kuskuren da masu mulki suke yi.

6. Ana ba wawaye manyan matsayi, attajirai kuwa ana ƙasƙantar da su.

7. Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, shugabanni kuwa suna tafiya a ƙasa kamar bayi.

8. Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara.

9. Wanda yake farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni. Wanda kuma yake faskare itace yana cikin hatsarinsu.

10. Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma hikima takan taimake shi ya ci nasara.

11. Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani.

12. Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi.

13. Farkon maganganunsa wauta ne, ƙarshensu kuma mugunta ne da hauka.

Karanta cikakken babi M. Had 10