Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 8:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba.

11. Gidiyon kuwa ya bi ta hanyar gefen hamada wadda take gabas da Noba da Yogbeha, ya faɗa wa rundunar, ta yadda ba su zato.

12. Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice.

13. Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres.

14. Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba'in da bakwai.

15. Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”

16. Ya kama dattawan garin Sukkot ya hukunta su da ƙayayuwa.

17. Ya kuma rushe hasumiyar Feniyel, ya karkashe mutanen birnin.

18. Sa'an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka kashe a Tabor?”Suka amsa, “Kamar yadda kake, haka suke. Suna kama da 'ya'yan sarki.”

19. Gidiyon ya ce musu, “Su 'yan'uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.”

Karanta cikakken babi L. Mah 8