Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 4:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al'ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira.

17. Amma Sisera ya gudu da ƙafa zuwa alfarwar Yayel matar Eber, Bakene, gama akwai jituwa tsakanin Yabin Sarkin Hazor da gidan Eber, Bakene.

18. Sai Yayel ta fito, ta taryi Sisera, ta ce masa, “Shigo nan, ubangijina, kada ka ji tsoro.” Ya kuwa bi ta zuwa cikin alfarwa, ta ɓoye shi bayan labule.

19. Ya ce mata, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa kaɗan in sha, gama ina jin ƙishi.” Ta kuwa buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, ta kuma lulluɓe shi.

20. Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar alfarwar, idan wani ya zo ya tambaye ki, ‘Ko akwai wani a nan?’ Sai ki ce, ‘Babu.’ ”

21. Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa'ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu.

Karanta cikakken babi L. Mah 4