Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 4:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Eber, Bakene kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za'anannim wanda yake kusa da Kedesh.

12. Aka faɗa wa Sisera cewa, Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa Dutsen Tabor.

13. Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al'ummai, har zuwa Kogin Kishon.

14. Debora ta ce wa Barak, “Tashi! Gama wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka, gama Ubangiji yana bi da kai!” Sai Barak ya gangaro daga Dutsen Tabor da mutum dubu goma (10,000) biye da shi.

15. Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa.

16. Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al'ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira.

17. Amma Sisera ya gudu da ƙafa zuwa alfarwar Yayel matar Eber, Bakene, gama akwai jituwa tsakanin Yabin Sarkin Hazor da gidan Eber, Bakene.

18. Sai Yayel ta fito, ta taryi Sisera, ta ce masa, “Shigo nan, ubangijina, kada ka ji tsoro.” Ya kuwa bi ta zuwa cikin alfarwa, ta ɓoye shi bayan labule.

19. Ya ce mata, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa kaɗan in sha, gama ina jin ƙishi.” Ta kuwa buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, ta kuma lulluɓe shi.

Karanta cikakken babi L. Mah 4